Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta yi cikakken bayani kan rahotannin sauye-sauyen da aka ce an yi wa wasu manyan jami’anta, da kuma kamfanonin da za su buga takardun zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce sauya wasu jami’ai a sassan gudanar da zaɓe, rajistar masu kaɗa ƙuri’a da fasahar sadarwa na buƙatar cikakken bayani domin tabbatar da bin ƙa’ida da kauce wa duk wani katsalandan na siyasa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma buƙaci INEC ta tabbatar ko ta musanta rahotannin da ke cewa kamfanin Hitech ko wani kamfani mai alaƙa da shi ya samu kwangilar buga wasu muhimman takardun zaɓe.
Atiku ya nemi hukumar ta bayyana sunayen dukkan kamfanonin da aka bai wa kwangiloli, ayyukan da kowannensu zai gudanar, da kuma matakan tsaro da za a ɗauka wajen buga takardun da adana su.
Ya jaddada buƙatar tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan matakan shirya zaɓen 2027, yana mai cewa ’yan Najeriya na da haƙƙin sanin yadda ake gudanar da shirye-shiryen zaɓen da za su tantance shugabanninsu.