Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn zaɓi ɗan Najeriya shugaban majalisar ƙungiyar masu noman kwakwar manja ta...

An zaɓi ɗan Najeriya shugaban majalisar ƙungiyar masu noman kwakwar manja ta duniya

An zaɓi shugaban Ƙungiyar Masu Samar da kwakwar manja ta Najeriya (NPPAN), Ambasada Alphonsus Inyang, a matsayin shugaban Majalisar Ƙungiyar Masu Ƙaramin Ƙarfi a Noman Kwakwar Manja ta Duniya (WCOPS).

An zaɓi shugaban Ƙungiyar Masu Samar da kwakwar manja ta Najeriya (NPPAN), Ambasada Alphonsus Inyang, a matsayin shugaban Majalisar Ƙungiyar Masu Ƙaramin Ƙarfi a Noman Kwakwar Manja ta Duniya (WCOPS).

An zaɓe shi ne yayin babban taron ƙungiyar da aka gudanar a Gabashin Kalimantan, Indonesia, inda mahalarta sama da 400 daga sassa daban-daban na duniya suka halarta.

Ƙungiyar WCOPS na da manufar kare haƙƙoƙi da bunƙasa harkokin masu ƙaramin ƙarfi a noman kwakwar manja a faɗin duniya, waɗanda adadinsu ya haura miliyan 50.

Inyang, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar mai kula da Afirka da Gabas ta Tsakiya, an zaɓe shi tare da wasu shugabanni daga Indonesia, Malaysia, Honduras da sauran ƙasashe.

Ya yi alƙawarin wakiltar Afirka yadda ya kamata, tare da kare muradun masu noman kwakwar manja da ƙarfafa ci gaban masana’antar a duniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments