Jiga-jigan jam’iyyar APC daga yankin Arewa ta Tsakiya sun shirya gudanar da babban gangamin siyasa a Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa, ranar Asabar, domin nuna goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, a zaɓen 2027.
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi A. Sule, ne zai karɓi baƙuncin gangamin, yayin da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, za ta halarta a matsayin babbar baƙuwa ta musamman.
Shirin gangamin ya biyo bayan wani taron jiga-jigan APC na Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 8 ga Oktoba, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe.
Taron ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, gwamnoni da mataimakansu, ministoci, ’yan majalisun tarayya da sauran manyan jami’an siyasa daga yankin.
Da yake jawabi bayan taron, Farfesa Yilwatda ya ce jiga-jigan jam’iyyar sun amince su haɗa kai wajen tattara magoya baya da ƙarfafa ayyukan siyasa a matakin ƙananan hukumomi domin tabbatar da nasarar gangamin da kuma tallafa wa takarar Tinubu da Shettima.
Ya bayyana taron da ake shirin gudanarwa a Lafiya a matsayin babban gangamin siyasa da zai nuna haɗin kan shugabannin APC na yankin Arewa ta Tsakiya.
A yayin taron na Abuja, shugaban APC ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu a haɗarin jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya a Jihar Ondo da kuma wani mummunan lamari da ya shafi haƙar ma’adinai a Jihar Neja.
Haka kuma, mahalarta taron sun yaba wa Sanata George Akume bisa ƙoƙarinsa na haɗa kan shugabannin siyasa daga sassa daban-daban na yankin, tare da gode wa Gwamna Abdullahi Sule kan amincewarsa ta karɓar baƙuncin gangamin.
Sun kuma tattauna shirye-shiryen halartar taron da shugabannin jam’iyya, ƙungiyoyin mata da matasa da sauran magoya baya daga jihohi shida na Arewa ta Tsakiya da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
An kammala taron ne da jaddada ƙudirin mahalarta na gudanar da gangamin Lafiya tare da nuna goyon bayansu ga sake zaɓen Tinubu da Shettima a 2027.