Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroSojoji sun kama ɗan siyasa a Yobe kan zargin taimaka wa ISWAP

Sojoji sun kama ɗan siyasa a Yobe kan zargin taimaka wa ISWAP

Ana zargin Mai Salati da yunƙurin ba sojoji cin hanci domin sakin wasu mutanen da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda.

Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun kama wani ɗan siyasa a jihar Yobe, Alhaji Wakiil Goni Mama, wanda aka fi sani da Mai Salati, bisa zargin ƙoƙarin taimaka wa ƙungiyar ’yan ta’addan ISWAP.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama ɗan siyasar ne bayan an gano zargin yunƙurinsa na ba sojoji cin hanci domin su saki wasu mutane da aka kama a garin Kanamma.

Rahoton da mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X ya nuna cewa kama Mai Salati ya biyo bayan binciken sirri da dakarun rundunar 27 Task Force Brigade suka gudanar.

An ruwaito cewa sojojin sun kama wasu mutane a Kanamma bisa zargin hannu wajen samar da kayayyakin tallafi ga ’yan ta’adda, inda aka fara gudanar da bincike a kansu.

A lokacin da ake binciken mutanen ne ake zargin Mai Salati ya yi ƙoƙarin shiga tsakani domin a sake su, tare da yunƙurin ba sojojin kuɗi don su sako su.

Sai dai rahoton ya ce dakarun sojin sun ƙi karɓar kuɗin da ake zargin ya yi ƙoƙarin ba su, maimakon haka suka kama shi tare da fara shirye-shiryen miƙa shi ga hukumomin da abin ya shafa domin ci gaba da bincike.

Daga bisani, an ɗauki Mai Salati da sauran waɗanda aka kama daga Damaturu zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin yi musu tambayoyi da gudanar da cikakken bincike.

Rahoton jaridar TheCable ya nuna cewa hukumomin tsaro na ƙoƙarin gano ko mutanen da aka kama suna da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci, da kuma irin gudunmawar da ake zargin sun bayar wajen taimaka wa ayyukansu.

Sai dai har yanzu zarge-zargen da ake yi wa Mai Salati ba su samu tabbaci ta hanyar hukuncin kotu ba, kuma ana buƙatar kammala bincike da bin hanyoyin shari’a domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments