Gwamnatin Faransa ta bayyana shirinta na taimaka wa Saudiyya wajen kare muhimman cibiyoyin makamashinta, musamman tashar mai ta Yanbu da bututun mai na East-West, yayin da ake ci gaba da fargabar hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa, Pascal Confavreux, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis, inda ya tabbatar da goyon bayan ƙasarsa ga Saudiyya kan matsalolin tsaro da take fuskanta.
Confavreux ya ce Faransa a shirye take ta shiga cikin matakan kariya domin kare muhimman kayayyakin makamashin Saudiyya, yana mai jaddada cewa za a yi hakan ne ta hanyar tsarin kariya mai tsauri.
Wannan mataki ya biyo bayan gargaɗin da mayakan Houthi na Yemen suka yi wa kamfanonin jiragen sama, inda suka yi barazanar cewa sararin samaniyar Saudiyya na iya zama wurin kai hare-haren soji.
A gefe guda, Saudiyya ta bayar da rahoton mutuwar mutane uku sakamakon hare-haren da aka kai filayen jiragen samanta ranar Laraba, ciki har da wani hari da ya shafi Riyadh, babban birnin ƙasar.
Matakin Faransa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan tsaron cibiyoyin makamashi da zirga-zirgar jiragen sama a yankin.