Direbobin manyan motoci sun toshe dukkan manyan hanyoyin shiga garin Bida a Jihar Neja, domin nuna rashin amincewarsu da mummunan yanayin hanyar Bida-Agaie-Lapai.
Direbobin, wadanda suka tare hanyoyin, sun ce sun dauki matakin ne saboda zargin gazawar gwamnati wajen fara aikin sake gina hanyar.
Daya daga cikin masu zanga-zangar, Buhari Aliyu, ya ce ya kamata gwamnati ko dai ta fara aikin sake gina hanyar Bida-Agaie-Lapai ko kuma ta bude wata hanyar Bida domin rage wahalhalun da masu ababen hawa ke fuskanta.
A cewarsa, yanayin hanyar ya tabarbare matuka, lamarin da ke haddasa lalacewar ababen hawa ko kifewarsu yayin da suke kokarin wucewa sassan da suka lalace.
“Idan gwamnati ba ta shirya sake gina hanyar Bida-Agaie-Lapai ba, su bude mana hanyar Bida domin mu bi.
“Hanyar ta lalace gaba daya. Motocinmu suna kifewa a kullum,” in ji Aliyu.
Shi ma wani direba, Suleiman Kaduna, wanda ya ce yana tafiya daga Kaduna zuwa Legas, ya bayyana cewa an toshe hanyar ne domin jawo hankalin gwamnatin tarayya kan halin da hanyar ke ciki.
“Har sai gwamnati ta fara aikin sake gina hanyar, ba za mu bude hanyar ba,” in ji shi.
Da aka tuntubi Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Kasa (FRSC) na Jihar Neja, Aishat Sa’adu, ta tabbatar da cewa hukumar ta gana da direbobin da ke zanga-zangar domin lallashe su su bude hanyar.
Sai dai ta ce kokarin nasu bai yi nasara ba, saboda masu zanga-zangar sun dage cewa sai sun gana da wakilin gwamnatin tarayya kafin su kawo karshen toshe hanyar.