Dan takarar gwamnan Jihar Adamawa na jam’iyyar SDP, Christopher Nathaniel, ya zaɓi Fauziyah Ahmed Rufai a matsayin abokiyar takararsa.
Ta haka Nathaniel ya bi sahun wani ɗan takara a jihar, Abdulrahman Haske na jam’iyyar APM, wanda shi ma ya riga ya bayyana mace, Safriel Glah, a matsayin abokiyar takararsa.
Nathaniel na jam’iyyar SDP ya bayyana Fauziyah Rufai a matsayin mataimakiyarsa a wani taro da ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga dukkan ƙananan hukumomi 21 na jihar zuwa Yola.
Nathaniel ya ce ya zaɓi Fauziyah Rufai ne saboda irin tarihin da take da shi wajen hidimar jama’a da kuma ƙwarewarta, yana mai fatan za ta kasance abokiyar haɗin gwiwa wajen samar da shugabanci mai mayar da hankali kan bukatun jama’a domin sauya yanayin ci gaban Jihar Adamawa.
Taron bayyana Fauziyah Rufai a matsayin mataimakiyar ɗan takarar gwamna ya samu halartar mambobin jam’iyyar NNPP reshen jihar, waɗanda suka bayyana cewa sun yanke shawarar haɗa tsarin jam’iyyarsu da na SDP.
Da yake magana a madadin masu goyon bayan NNPP, Mustapha Mohammed Abbo ya ce matakin da suka ɗauka na haɗa kai, musamman wajen yaƙin neman zaɓen ɗan takarar SDP na gwamna, ya samo asali ne daga amincewarsu da manufofin da ya gabatar a cikin kundin shirinsa na mulki.