Saturday, October 17, 2026
HomeWasanniA rana irin ta yau, FIFA ta dakatar da Najeriya daga buga...

A rana irin ta yau, FIFA ta dakatar da Najeriya daga buga wasa

Magoya baya sun shiga fargabar cewa ƙasar za ta rasa damar shiga wasu manyan wasanni na duniya.

A ranar 4 ga Oktoba, Shekarar 2010, Najeriya ta fuskanci wani abin kunya a tarihin ƙwallon ƙafarta, bayan hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, ta dakatar da ƙasar daga shiga duk wata fafatawar ƙwallon ƙafa ta duniya.

Matakin na FIFA ya zo ne kwanaki kaɗan bayan kammala gasar Kofin Duniya na Shekarar 2010 da aka gudanar a Afirka ta Kudu.

Super Eagles ta kasa samun nasara a gasar, inda ta fice tun daga matakin rukuni bayan samun maki ɗaya kacal.

Bayan dawowar tawagar daga gasar, gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta janye Super Eagles daga wasannin duniya na tsawon shekaru biyu, tana mai cewa tana son a yi gyare-gyare a harkar ƙwallon ƙafa ta ƙasar.

Sai dai wannan mataki bai yi wa FIFA daɗi ba. Hukumar ta FIFA ta dage cewa gwamnatoci ba su da ikon tsoma baki kai tsaye cikin harkokin gudanar da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasashensu.

A cewar FIFA, ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ya kamata su kasance masu cin gashin kansu ba tare da katsalandan daga gwamnati ba.

Saboda haka, a ranar 4 ga Oktoba, 2010, FIFA ta sanar da dakatar da Najeriya daga dukkan wasannin ƙwallon ƙafa na duniya har sai an warware matsalar.

Dakatarwar ta jefa ƙwallon ƙafar Najeriya cikin wani yanayi mai ɗaukar hankali, musamman ganin yadda Super Eagles ta kasance ɗaya daga cikin fitattun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Afrika.

Magoya baya sun shiga fargabar cewa ƙasar za ta rasa damar shiga wasu manyan wasanni na duniya.

Sai dai matsin lamba daga FIFA da kuma bukatar Najeriya ta ci gaba da shiga gasannin ƙasa da ƙasa ya sa aka fara neman mafita cikin gaggawa.

Daga bisani, gwamnatin Najeriya ta ja da baya daga matakan da FIFA ta yi adawa da su, lamarin da ya buɗe ƙofa ga dawo da Najeriya cikin harkokin ƙwallon ƙafa na duniya.

Wannan lamari ya zama darasi mai muhimmanci a tarihin ƙwallon ƙafa ta Najeriya, domin ya nuna irin tsananin matsayar FIFA kan ‘yancin hukumomin ƙwallon ƙafa daga tsoma bakin gwamnati.

Shekaru 16 bayan wannan lamari, 4 ga Oktoba na ci gaba da tunasar da masoya ƙwallon ƙafa game da ranar da Najeriya ta shiga rikici da babbar hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments