An kashe shugaban jam’iyyar NDC na mazaɓar Fiidi da ke ƙaramar hukumar Makurɗi ta jihar Benue, Igbu Job Terhemen, bayan wasu da ba a san ko su wanene ba sun kai masa hari.
Rahotanni sun ce maharan sun ɗaure Terhemen da igiya tare da yi masa allurar wani sinadari da ake zargin mai guba ne, kafin su jefar da shi a wani daji da ke kusa da gidansa da misalin ƙarfe 2 na dare.
An gano shi cikin mawuyacin hali, amma ya rasu kafin a kai shi asibiti domin samun kulawar lafiya.
Bayan faruwar lamarin, jam’iyyar NDC ta buƙaci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike domin gano tare da cafke waɗanda ake zargi da hannu a kisan.
Sai dai kakakin ’yan sandan jihar Benue, DSP Peter Aondongu, ya ce rundunar ba ta samu rahoton kisan ba har zuwa lokacin da rahoton ya samu.