Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaGombe 2027: ’Yan takara sun ƙalubalanci shigar Pantami sabon zaɓen PDP

Gombe 2027: ’Yan takara sun ƙalubalanci shigar Pantami sabon zaɓen PDP

Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na ɗan takarar gwamna a ranar Talata, bisa umarnin da Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta bayar.

Kotun ta soke sakamakon zaɓen fidda gwani na baya wanda ya samar da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan PDP, tare da umartar jam’iyyar da ta sake gudanar da zaɓen.

Sai dai yayin sabon zaɓen, ’yan takara biyu, Usman Aliyu Garry Kogunan Gombe da Khamisu Ahmed Mailantarki, sun nuna adawa da shigar Pantami cikin sabon tsarin zaɓen.

Mailantarki ya yi iƙirarin cewa babu wani ɓangare na umarnin kotun da ya ce Pantami ya shiga sabon zaɓen, yana mai cewa shi ne sahihin ɗan takarar gwamnan PDP a jihar.

“Babu inda aka ce Pantami ya shiga sabon zaɓen fidda gwani. Ni ne sahihin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Gombe,” in ji Mailantarki.

A baya dai PDP ta sanar da tantance Pantami, Mailantarki da Usman Aliyu Garry tare da bayyana cewa sun cancanci shiga sabon zaɓen fidda gwani.

Sabon takaddamar ta ƙara jawo ce-ce-ku-ce kan tsarin zaɓen fidda gwamni na PDP a Gombe, musamman kan cancantar ’yan takarar da kuma wanda zai samu tikitin jam’iyyar a hukumance.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments