Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaAtiku ya sake neman a saki El-Rufai da sauran fursunonin siyasa

Atiku ya sake neman a saki El-Rufai da sauran fursunonin siyasa

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya sake neman a gaggauta sakin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna kuma Mataimakin Shugaban Kwamitin Yaƙin neman zaɓen ADC, Malam Nasir El-Rufai, da sauran mutanen da ya bayyana a matsayin fursunonin siyasa.

Atiku ya yi wannan kiran ne ranar Laraba lokacin da ya karɓi shugabannin ADC na Jihar Kaduna a gidansa da ke Abuja.Wannan na kunshe a cikin sanarwa mai dauke da sa hannun Kola Ologbondiyan, Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’aKwamitin Yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC.

Atiku ya ce gwamnatin tarayya ba ta da wani dalili na ci gaba da tsare ’yan ƙasa saboda ra’ayoyinsu na siyasa ko alaƙarsu da wata ƙungiyar siyasa.

“Gwamnatin Tarayya ba ta da wani dalili na ci gaba da tsare mutane bisa dalilin imaninsu ko alaƙarsu da siyasa. Mu yi fatan gwamnatin tarayya za ta saurari shawarwari masu kyau ta sake su nan take,” in ji Atiku.

Da yake magana kan dadaddiyar alaƙarsa da Jihar Kaduna, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce a tsawon lokaci ya samu gagarumin goyon baya daga al’ummar jihar, yana mai jaddada cewa Kaduna za ta kasance muhimmiyar jiha ga ADC a babban zaɓen 2027.

“Jihar Kaduna za ta kasance muhimmiyar jiha a duk abin da za mu yi. Ina kuma son jam’iyyarmu ta lashe Jihar Kaduna. Kada mu bari a sace mana zaɓe a jihar ko a kowace jiha,” in ji shi.

Atiku ya kuma bukaci shugabanni da magoya bayan ADC a jihar da su koyi darasi daga zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar kwanan nan, inda ya yi zargin cewa masu zaɓe sun ƙi karɓar kuɗin da aka ba su domin sayen ƙuri’unsu, suka kuma zaɓi ‘yan takara bisa ra’ayinsu.

“Dukkanmu za mu iya tuna abin da ya faru a Jihar Osun. Babu kuɗin da ba a kai jihar ba, haka kuma an kai dukkan jami’an tsaro. Amma mutanen Osun sun karɓi kuɗinsu kuma suka ƙi zaɓensu,” ya ƙara da cewa.

Tun da farko, Shugaban Kwamitin Yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC, Malam Kashim Imam, ya bayyana cewa Jihar Kaduna ce ke kan gaba a aikin rajistar sabbin mambobin jam’iyyar da ake gudanarwa a faɗin ƙasar, kuma har yanzu tana ci gaba da riƙe wannan matsayi.

Imam ya buƙaci shugabannin jam’iyyar a jihar da su mayar da yawan mambobin da suka samu zuwa gagarumin goyon bayan ƙuri’a ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2027.

“Jihar Kaduna ce ta zo ta farko wajen rajistar mambobin jam’iyya kuma ta ci gaba da riƙe wannan matsayi. Jihar Kaduna dole ta samar da aƙalla ƙuri’a miliyan ɗaya ga ɗan takarar shugaban ƙasarmu. Kaduna na da muhimmiyar rawa ga ADC gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027,” in ji Imam.

A nasa jawabin na buɗe taron, ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna na ADC, Alhaji Isah Ashiru, ya bayyana kwarin gwiwa kan makomar jam’iyyar, yana mai cewa ADC a shirye take ta lashe zaɓen gwamnan jihar tare da samun nasarar dukkan ’yan takararta a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments