Kwafin hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ya nuna cewa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami na da damar shiga sabon zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP a jihar, bayan kotun ta soke tsarin da ya samar da shi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
A hukuncin da Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ta yanke, kotun ta umarci PDP da gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani, bayan da aka ƙalubalanci yadda Pantami ya samu tikitin jam’iyyar a zaɓen da aka gudanar a watan Mayu.
Sai dai kwafin hukuncin ya nuna cewa kotun ba ta amince da buƙatar hana Pantami sake shiga takarar ba.
A cikin ƙalubalen da aka gabatar, an yi zargin cewa Pantami ya koma PDP ne bayan ya kasance ɗan jam’iyyar APC, amma kotun ba ta ga hujjar da za ta tabbatar da wannan zargin har ta kai ga hana shi shiga sabon zaɓen ba.
Hakan na nufin Pantami na cikin waɗanda za su iya fafatawa a sabon zaɓen, tare da wasu masu neman tikitin PDP, ciki har da Khamisu Ahmed Mailantarki da Usman Aliyu Garry.
Rahotanni sun ce PDP ta sanya ranar 29 ga Satumba 2026 domin gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani a Gombe.
Sabon zaɓen ya biyo bayan hukuncin kotun da ya soke zaɓen fitar da gwani na ranar 26 ga Mayu 2026, tare da umartar PDP da ta koma ta gudanar da sabon zaɓe bisa ƙa’idojin jam’iyyar da dokokin zaɓe.