Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiNajeriya ta buƙaci kujeru biyu na dindindin ga Afirka a Majalisar Tsaron...

Najeriya ta buƙaci kujeru biyu na dindindin ga Afirka a Majalisar Tsaron UN

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci a bai wa Afirka kujeru biyu na dindindin a Majalisar Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya, tare da cikakken iko da nauyin da ke tattare da zama mamba, ciki har da ikon amfani da karfin iko.

Tinubu ya bayyana hakan a jawabinsa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya gabatar a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 a New York, inda ya ce tsarin rabon iko na shekarar 1945 bai dace da duniyar 2026 ba.

Ya kuma nemi a bai wa Afirka kujeru biyar na wucin-gadi, yana mai cewa nahiyar ba za ta ci gaba da kasancewa a wajen manyan shawarwarin da suka shafi duniya ba, duk da yawan batutuwan da suka shafe ta a Majalisar Tsaro.

A wani ɓangare na jawabin, Tinubu ya yi kira da a kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe da ƙara ƙarfafa diflomasiyya, dokokin ƙasa da ƙasa da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe.

Haka kuma, ya jaddada buƙatar tallafin kuɗi da fasaha ga ƙasashe masu tasowa wajen yaƙi da sauyin yanayi, tare da ƙara samar da makamashi da rage talauci ba tare da yin watsi da manufofin kare muhalli ba.

Tinubu ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da amfani da fasahar AI, bunƙasa hanyoyin sadarwa da harkokin kasuwancin fasaha, yayin da ta nemi sauya tsarin kuɗaɗen duniya domin ƙasashe masu tasowa su samu sauƙin samun kuɗaɗen ci gaba.

A fannin tsaro kuwa, ya ce yaƙi da ta’addanci da sauran barazanar tsaro na buƙatar haɗin gwiwar ƙasashe, ilimi, damar tattalin arziki da shugabanci na gari, tare da jaddada aniyar Najeriya na ci gaba da taka rawa wajen samar da zaman lafiya a Afirka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments