Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaPantami da ɗan takarar APC sun shirya kece raini a wata muhawara...

Pantami da ɗan takarar APC sun shirya kece raini a wata muhawara a Gombe

’Yan takarar kujerar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyun PDP da APC, Farfesa Isa Ali Pantami da Dr. Jamil Isyaku Gwamna, sun bayyana shirinsu na shiga muhawara domin tattauna tsare-tsare da makomar jihar gabanin zaɓen 2027.

Rahoton Legit.ng ya ce mai magana da yawun Jamilu Gwamna, Ibrahim Sani Shawai, ya bayyana cewa ɗan takarar na APC a shirye yake ya fuskanci sauran masu neman kujerar gwamnan domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban Gombe.

Shawai ya ce Jamilu a shirye yake ya halarci muhawarar a kowace rana, yana mai cewa ya kamata tattaunawar ta mayar da hankali kan ƙwarewar ’yan takara, gogewarsu da sakamakon ayyukan da suka gudanar, maimakon zarge-zarge da farfagandar siyasa.

Ya ƙara da cewa muhawarar ya kamata ta shafi muhimman batutuwa da suka haɗa da ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi, noma, ruwa, ababen more rayuwa, zuba jari da bunƙasa masana’antu.

A nasa ɓangaren, ɗan takarar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, shi ma ya amince da kiran gudanar da muhawarar.

Sanarwar da ƙungiyar Pantamiyya Movement ta fitar ta ce Pantami na son a buɗe muhawarar ga al’ummar Gombe, tare da watsa ta kai tsaye ta kafafen yaɗa labarai domin jama’a su saurara su kuma tantance tsare-tsaren ’yan takara.

Sanarwar ta bayyana cewa Pantami ya nuna shirinsa na halartar muhawarar tun ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, da ƙarfe 10 na safe, muddin sauran ’yan takara ma suna a shirye.

Ya kuma buƙaci a mayar da hankali kan manufofi, ƙwarewa da sakamakon ayyuka da za a iya aunawa, ba zagi ko kalaman siyasa marasa tushe ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments