Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa jami’an ƙasarsa da na Iran sun gudanar da tattaunawa mai kyau a birnin New York, yayin da rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu ke shiga wata na bakwai.
Trump ya bayyana hakan ne bayan jawabin da ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya nuna cewa har yanzu akwai yiwuwar Amurka da Iran su cimma matsaya ta hanyar yarjejeniya.
Rahotanni sun ce wakilan ƙasashen biyu sun gana na tsawon sa’o’i uku a ranar Talata, duk da cewa ba a bayyana cikakken bayani kan abubuwan da suka tattauna ba.
A nasa ɓangaren, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce ƙasarsa ta isar wa Amurka sharuddan da take buƙata domin kawo ƙarshen rikicin, ta hannun masu shiga tsakani daga Qatar.
Daga cikin buƙatun Iran akwai dakatar da hare-haren Amurka da killacewar ruwan teku, cire takunkuman da aka kakaba mata, da kuma sakin kadarorinta da aka daskarar.
Baghaei ya ce matsayar ƙasarsa kan mashigar ruwan Hormuz da tsaron yankin ba ta sauya ba.
Sai dai Trump ya jaddada cewa Iran ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, tare da kira da a sake buɗe mashigar ruwan Hormuz gaba ɗaya.