Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiKACRAN ta bukaci NEDC ta hada kai da gwamnonin Arewa wajen samar...

KACRAN ta bukaci NEDC ta hada kai da gwamnonin Arewa wajen samar da ayyukan yi

Kungiyar ta ce hadin gwiwar zai taimaka wajen bunkasa noma, samar da ayyukan yi da gano albarkatun kasa.

Kungiyar KACRAN ta bukaci Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas (NEDC) da ta hada kai da gwamnonin yankin domin samar da ayyukan yi, bunkasa noma da kuma gano albarkatun kasa.

KACRAN ta bayyana NEDC a matsayin daya daga cikin hukumomin gwamnatin tarayya da suka taka muhimmiyar rawa wajen sake gina Arewa maso Gabas, musamman bayan barnar da hare-haren ’yan tada kayar baya suka haifar.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ta kasa, Hon. Khalil Mohd Bello, ya sanya wa hannu, KACRAN ta ce NEDC ta gina da gyara makarantu, gidaje, ofisoshi, tituna, magudanan ruwa da gadoji a sassan yankin.

Kungiyar ta kuma ce hukumar ta taimaka wajen horas da dubban mutane kan sana’o’i domin su samu damar dogaro da kansu da kuma samar da ayyukan yi.

KACRAN ta ce samar da ayyukan yi ga matasa, musamman wadanda suka kammala jami’o’i da kwalejoji, zai taimaka wajen rage yiwuwar shiga ayyukan laifi tare da ba su damar bayar da gudunmawa wajen ci gaban yankin.

Game da noma kuwa, kungiyar ta bukaci a kara mayar da hankali kan noman amfanin gona, kiwo da kamun kifi domin kara samar da abinci da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje.

KACRAN ta ce NEDC za ta iya samar da kwararru da tallafin kudi, yayin da gwamnonin jihohin yankin za su samar da filaye da tsaro domin gudanar da ayyukan.

Kungiyar ta kuma yi kira da a fara bincike da sarrafa albarkatun kasa da ke yankin Arewa maso Gabas, domin bunkasa masana’antu da kara samun kudaden shiga ga Najeriya.

KACRAN ta ce irin wannan hadin gwiwa zai iya zama abin koyi ga sauran hukumomin raya yankuna a Najeriya.

Kungiyar ta yaba wa NEDC kan shirinta na samar da motocin sufuri 10,000, ciki har da manyan motocin haya, motocin fasinja 18, tasi da kekunan Keke-NAPEP domin saukaka sufuri ga jama’a.

KACRAN ta kuma yabawa Manajan Daraktan NEDC, Alhaji Mohammed Goni Alkali, da Daraktan Gudanarwa da Kudi, Dr. Garba Iliya, tare da sauran shugabanni da ma’aikatan hukumar kan ayyukan da suke gudanarwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments