Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce a halin yanzu ba ta da wani shirin ƙara kuɗin wutar lantarki da ’yan ƙasa ke biya.
Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa gwamnatin ta fi mayar da hankali wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma daidaita harkokin ɓangaren makamashin ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ministan yana cewa gwamnati na kuma ƙoƙarin magance matsalolin kuɗi da sauran ƙalubalen da suka addabi ɓangaren wutar lantarki.
Ya ce waɗannan matakai na daga cikin kokarin gwamnati na ganin an samu ingantaccen tsarin samar da wutar lantarki ba tare da ƙara wa ’yan Najeriya wani nauyin kuɗi a halin yanzu ba.