Ladanin Masallacin Harami da ke birnin Makkah, Sheikh Ibrahim bin Adel Hamzah Al-Madani, ya rasu a safiyar Litinin, 21 ga Satumba, 2026, yana da kimanin shekaru 48 a duniya.
Marigayin ya shafe shekaru yana kiran sallah a Harami, inda muryarsa ta zama sananniya ga al’ummar Musulmi da dama a faɗin duniya.
An haifi Sheikh Ibrahim a Madina, inda ya fara kiran sallah yana ɗan shekara 15 a wani masallaci.
Daga bisani, ya zama ladani a Masallacin Al-Maddah, kafin daga baya a naɗa shi cikin ladanan Masallacin Harami a watan Ramadan na shekarar 1439H, wato 2018.
An bayyana marigayin a matsayin mutum mai yawan ibada da sadaukarwa, wanda ya haɗa salon kiran sallar Madina da na Makkah.
Rahotanni sun ce za a yi sallar jana’izarsa a Masallacin Harami, sannan a binne shi a makabartar Jannatul Mu’alla da ke Makkah.