Ofishin Jakadancin Amurka a Iran ya gargaɗi ‘yan ƙasar Amurka da ke Iran da su fice daga ƙasar cikin gaggawa, sakamakon ƙara taɓarɓarewar yanayin tsaro da kuma barazanar sake barkewar rikici a yankin.
Ofishin ya kuma shawarci Amurkawa da su guji zuwa Iran ko da kuwa saboda wani dalili, yana mai gargaɗin cewa ana iya soke tashin jiragen sama ko kuma rufe sararin samaniyar ƙasar, wanda ka iya kawo cikas ga ficewar waɗanda ke son barin ƙasar.
Gargadin ya zo ne a daidai lokacin da Amurka da Iran ke ci gaba da fuskantar takun-saka, duk da alamun yiwuwar komawa teburin tattaunawa ta hanyar masu shiga tsakani daga Pakistan da Qatar.
A gefe guda, jami’an Iran sun bayyana cewa ƙasar na shirye-shiryen tattaunawa ta diflomasiyya, amma kuma a shirye take ta tunkari duk wani sabon rikici idan aka sake samun tashin hankali.