Dubban mazauna wasu sassan Jihar Sokoto da suka tsere daga gidajensu saboda hare-haren ’yan bindiga na fuskantar sabon ƙalubalen samun matsuguni da abinci a wuraren da suka koma.
Wasu daga cikin mutanen sun ce suna biyan makudan kudade wajen haya, yayin da wasu ke rayuwa a sansanonin ’yan gudun hijira da makarantu. A Gummi ta Jihar Zamfara, wasu sun ce haya na iya kaiwa N500,000 a shekara, yayin da a Tureta ake biyan N100,000 a wata kan gida mai dakuna uku.
Wani ɗan kasuwa, Umar Abubakar, ya ce ’yan bindiga sun kashe ɗan’uwansa tare da kona gidansu da shagon da yake sana’a, lamarin da ya janyo masa asarar kusan N1.5m. Ya ce ya sayar da wasu dabbobinsa domin biyan N250,000 na hayar gida na tsawon watanni shida.
A Sabon Birni, wasu mutanen da suka rasa gidaje, gonaki da sana’o’insu sun koma aikin yi na wucin gadi domin samun abin da za su ci. Wasu kuma na tattara itace da ciyawa suna sayarwa, yayin da karatun ’ya’yan wasu iyalai ya tsaya sakamakon gudun hijira.
A Goronyo kuwa, wasu mazauna sansanin ’yan gudun hijira sun shafe shekaru da dama ba tare da komawa garuruwansu ba. Shugaban wani sansani, Yakubu Adamu, ya ce sansanin na dauke da mutane 5,764 a watan Maris 2026, kuma adadin ya ƙaru tun daga lokacin.
Mazauna yankunan sun ce rashin tsaro ne ya fi hana su komawa gidajensu, inda suka bukaci jami’an tsaro su ƙara kai hare-hare zuwa maboyar ’yan bindiga tare da dawo da tsaro a garuruwansu.
Wani masanin tsaro, Dr Yahuza Ahmad Getso, ya ce ƙara kai farmaki maboyar ’yan bindiga, inganta tattara bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’umma na daga cikin hanyoyin da za a iya magance matsalar.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da shugabannin ƙananan hukumomi, sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa kai wajen samar da tsari na dindindin domin dawo da tsaro da kuma mayar da mutanen da suka rasa matsugunansu gidajensu.