Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya kori ɗaya daga cikin manyan hadimansa kan harkokin majalisa, King Indara.
An dakatar da Indara ne bisa zargin wallafa wasu saƙonni a kafafen sada zumunta da ake cewa sun ƙunshi kalaman rashin girmamawa ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Shitu Madaki Kunchi, babban mataimakin Barau kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, ne ya bayyana matakin cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin Sanatan ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan wasu rubuce-rubuce da saƙonni da aka danganta da Indara a kafafen sada zumunta, ciki har da wani saƙo mai taken “Abba Must Go”.
Kunchi ya ce an ɗauki saƙonnin a matsayin kalaman da suka nuna rashin girmamawa da rashin da’a ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Sanarwar ta ƙara da cewa abin da Indara ya yi ya saɓa wa ƙa’idojin jam’iyyar APC, musamman umarnin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na tallafawa da kare jam’iyyar daga sama har ƙasa.
“Irin wannan ɗabi’a ta saɓa wa ƙa’idoji da tarbiyyar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, da kuma manufofin jam’iyyar APC, musamman umarninsa na tallafawa da kare jam’iyyar daga sama har ƙasa,” in ji sanarwar.