Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta bayyana cewa gwamnatin Saudiyya ba ta amince da buƙatar Najeriya na ƙarin guraben Aikin Hajji a shekarar 2027 ba.
NAHCON ta ce ta tattauna da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya kan buƙatar ƙara adadin guraben, sakamakon yawaitar Musulman Najeriya da ke son sauke faralin Aikin Hajji.
Hakan ya biyo bayan buƙatun ƙarin gurabe da hukumomin Aikin Hajji na wasu jihohin ƙasar suka gabatar.
Sai dai Saudiyya ta bar adadin guraben Najeriya kamar yadda yake, inda aka ware gurabe 35,000 ga alhazan da za su tafi ƙarƙashin gwamnati, yayin da kamfanonin Aikin Hajji masu zaman kansu da ke da lasisi aka ware wa 15,000.
Hakan ya sanya jimillar adadin guraben da Najeriya za ta samu a Aikin Hajjin 2027 ya kasance 50,000.