China ta roƙi Iran da ta yi amfani da tasirinta wajen shawo kan ƙungiyar Houthi ta Yemen, bayan Saudiyya ta nemi taimakon Beijing kan ƙara tsanantar hare-haren ƙungiyar a yankin Bahar Maliya da mashigar Bab el-Mandeb.
Majiyoyi uku daga Iran da ke da masaniya kan lamarin ne suka bayyana hakan ga Reuters, inda suka ce Saudiyya ta nemi China ta taimaka wajen dakile barazanar da ci gaban Houthi ke haifarwa ga hanyoyin jigilar man fetur da kayayyaki.
Rahoton ya ce China ta bayyana a bainar jama’a cewa tana kira da a yi ƙoƙarin rage tashin hankali, a koma tattaunawa, sannan a tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa.
Sai dai majiyoyin sun ce saƙon sirrin da Beijing ta aika wa Tehran ya fi wannan matsayi na jama’a kai tsaye, inda ta bukaci Iran ta yi amfani da tasirinta kan Houthi.
A cewar majiyoyin, martanin Iran shi ne cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin ba za su samu ba matuƙar ana ci gaba da yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran.
Sai dai babu wata alama da ke nuna cewa China ta yi barazanar ɗaukar matakin tattalin arziki kan Iran idan ba ta yi amfani da tasirinta kan Houthi ba.