Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ta fara bincike kan wani mutum mai suna Usaini Ibrahim, wanda ake zargi da kama shi da jabun kuɗin Amurka da yawansu ya kai $212,200.
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ne suka kama Usaini a ranar 3 ga Satumba, 2026, a kan titin Maiduguri da ke Kano, bayan da suka gano jabun kuɗin.
Daga bisani, NDLEA ta miƙa wanda ake zargin da jabun kuɗin ga EFCC domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.
An gudanar da miƙa mutumin a hukumance a ofishin EFCC da ke Kano, inda Mukaddashin Daraktan Shiyyar Kano, Mataimakin Kwamandan EFCC na aji na ɗaya (ACE I), Friday S. Ebelo, ya karɓi wanda ake zargin da kayayyakin da aka kama.
Da yake jawabi, Ebelo ya gargadi jama’a kan zamba, yana mai cewa ana yawan amfani da jabun kuɗi wajen yaudarar mutanen da ba su sani ba.
“Shigowar irin waɗannan jabun kuɗaɗen cikin tattalin arzikin ƙasa ba abu ne mai kyau ba,” in ji shi.
Ya buƙaci jama’a su kasance masu taka-tsantsan tare da guje wa mutanen da ke yi musu tayin “ninka masu kuɗi” ko shiga wasu harkokin kuɗi ta hanyoyin da ba su dace ba.
A halin yanzu, wanda ake zargin yana tsare a hannun EFCC, kuma ana sa ran gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.