Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani fitaccen ‘dan TikTok, Ukasha Yahaya, wanda aka fi sani da UK International, kan wasu bidiyoyin da ke nuna shi tare da mata suna aikata badala.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dakta Mujahid Aminuddeen, ya tabbatar da kama Ukasha a ranar Alhamis, inda ya ce an cafke shi ne bayan hukumar ta samu bayanan sirri cewa ya shigo Kano.
Ya ce a halin yanzu ana tsare da shi yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Ukasha, ɗan asalin Gusau ne a Jihar Zamfara, amma yana zaune a Abuja. A yayin tambayoyi, ya amsa cewa ba zai iya tuna adadin bidiyoyin da ya shirya tare da mata ba.
Wasu daga cikin bidiyon sun nuna shi yana rawa, rungumar mata ko ɗaukar su, yayin da wasu ke nuna wuraren iyo da kuma wanka.
Ukasha ya bayyana cewa wasu daga cikin bidiyonsa sun samu kallon mutane tsakanin miliyan ɗaya zuwa uku.
Da aka tambaye shi yadda yake samun matan da suke fitowa a bidiyon, ya ce su ne suke tuntuɓarsa saboda ya sanya su a cikin bidiyoyinsa.
Haka kuma, lokacin da aka tambaye shi ko zai iya saka ’yan uwansa mata cikin irin waɗannan bidiyoyi, ya ce dukkansu sun yi aure, sannan mahaifiyarsa da wasu mutane da dama sun sha yi masa nasiha kan abin da yake yi.
Ya kuma bayyana cewa yana tunanin daina irin wannan badala, musamman yayin da yake shirin yin aure.
Ukasha ya nemi afuwa tare da yin alkawarin cewa ba zai sake aikata irin hakan ba.
Dakta Mujahid ya ce za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
Ya kuma gargadi matasa da su guji amfani da TikTok wajen yada abubuwan da suka saɓa wa ɗabi’a da koyarwar addini.