Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da buƙatar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, na isar da takardun kotu ga Shugaba Bola Tinubu ta hannun jam’iyyar APC.
Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya bayar da umarnin a ranar Laraba, yayin da yake yanke hukunci kan wata buƙata da lauyan Atiku, O.T. Omotayo-Ojo, ya shigar, yana neman kotu ta ba da damar yin amfani da hanyar isar da takardu ta madadin kai tsaye ga wanda ake ƙara.
Atiku da jam’iyyarsa ta ADC sun shigar da ƙara suna neman a hana Tinubu da APC shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bisa zargin cewa an gabatar wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) takardar shaidar kammala hidimar NYSC da ake zargin an jirkita.
Ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026 ta sanya Tinubu a matsayin wanda ake ƙara na farko, APC na biyu, sannan INEC na uku.
Masu ƙarar na kuma neman kotu ta umarci INEC ta cire sunayen Tinubu da APC daga jerin ‘yan takara da jam’iyyun siyasa da za su shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A yayin gabatar da buƙatar a ranar Laraba, Omotayo-Ojo ya shaida wa kotun cewa ya zama dole a nemi wannan umarni saboda masu ƙarar sun kasa kai wa Tinubu takardun ƙarar da kansu.
Saboda haka, ya roƙi kotun ta ba su damar isar da takardun ta hannun APC, wadda ita ce jam’iyya ta biyu da ake ƙara.
Mai shari’a Ekwo ya amince da buƙatar. Bayan lauyan ya yi alƙawarin cewa za a kammala isar da takardun cikin kwanaki bakwai, kotun ta bayar da umarnin hakan.
Daga nan sai kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Satumba domin ci gaba da duba lamarin.