Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bukaci jami’ar UNN ta fitar da dukkan bayanan karatunsa domin jama’a su duba, yana mai cewa “ba ni da abin boyewa.”
Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da 90 Minutes Africa, inda ya ce bai san yana da wani fayil a FBI ba, kuma bai taba mu’amala da hukumar ba.
Ya bukaci UNN ta fitar da bayanan shigarsa jami’a da sakamakon jarabawarsa daga shekarar farko har zuwa kammala karatu. Haka kuma ya nemi sauran makarantun da ya halarta su bayyana bayanansa.
Obi ya ce duk mai neman mukamin gwamnati ya kamata ya kasance a shirye domin a binciki tarihin rayuwarsa da bayanansa, yana mai kira ga sauran ’yan takarar shugaban kasa su yi hakan.
Batun bayanan karatun Obi ya sake daukar hankali bayan Abayomi Arabambi ya shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, yana neman a tilasta wa UNN ta fitar da takardun karatunsa karkashin dokar Freedom of Information Act.