Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta taya Maryam Ibrahim Dan’Azumi murnar lashe gasar karatun Alƙur’ani ta duniya da aka gudanar a Makka, Saudiyya.
Maryam ta lashe gasar mata a karo na 46 na gasar Sarkin Abdulaziz ta ƙasa da ƙasa ta karatun Alƙur’ani. A yayin tarbar da aka yi mata a Abuja ranar Talata, Uwargida Tinubu ta ba ta kyautar Naira miliyan 20.
Oluremi Tinubu ta ce nasarar Maryam abin alfahari ce ga Najeriya da ’ya’ya mata a faɗin duniya, tare da bayyana ta a matsayin abin koyi ga sauran mata.
Ta kuma yaba wa iyayen Maryam bisa yadda suka tallafa mata wajen karatu da haɓaka baiwarta, tana mai cewa nasarar ta ɗaukaka sunan Najeriya a duniya.
Mahaifin Maryam, Ibrahim Dan’Azumi, da Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, tare da wasu jami’an gwamnatin jihar, sun raka ta yayin ziyarar.