Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiBayan sace malamai maza, malaman addini mata na Arewa sun goyi bayan...

Bayan sace malamai maza, malaman addini mata na Arewa sun goyi bayan Tinubu a zaben 2027

Wasu malaman addinin Musulunci mata daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kaduna, inda ya ce malaman matan sun yanke wannan shawara ne bisa ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gudanar a sassa daban-daban na ƙasar.

A cewarsa, goyon bayan da malaman matan suka bayar ba wai saboda wata manufa ta kashin kai ba ce, illa saboda irin nasarorin da suka ce gwamnatin Tinubu ta samu musamman a fannoni kamar ilimi, kiwon lafiya, noma da ayyukan more rayuwa.

Uba Sani ya ƙara da cewa malaman matan sun yaba da yadda gwamnatin Tinubu ke ƙoƙarin bai wa yankuna daban-daban damar cin gajiyar shirye-shiryen gwamnati ba tare da nuna bambanci ba.

Ya kuma ambaci shirye-shiryen Asusun Ba da Lamunin Ilimi ga Ɗaliban Najeriya, wato NELFUND, da kuma shirye-shiryen koyar da sana’o’i da fasahohi na TVET, yana mai cewa yankin Arewa ya amfana sosai da waɗannan shirye-shirye.

Gwamnan ya ce goyon bayan malaman matan ya nuna yadda wasu sassa na al’ummar Arewa ke kallon ayyuka da manufofin gwamnatin Tinubu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments