Sashen Leken Asirin Kuɗi na Najeriya (NFIU) ya ce ya fara shirye-shiryen kafa wani tsarin haɗin gwiwa na musayar bayanan leƙen asirin kuɗi.
Hakan na zuwa ne yayin da sashen ya tattara hukumomin sa ido, bankuna, kamfanonin inshora, kamfanonin fintech, masu ba da hidimomin kadarorin zamani (Virtual Asset Service Providers), kamfanonin fasaha da sauran masu ruwa da tsaki domin gano sabbin barazanar kuɗi da dakile hanyoyin sadarwar safarar kuɗaɗen haram.
Hukumar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis cewa matakin na da nufin ƙarfafa musayar bayanan leƙen asirin kuɗi tsakanin hukumomin gwamnati da cibiyoyi masu zaman kansu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwanan nan NFIU ta gano wata sabuwar hanyar tara kuɗi daga jama’a da ake amfani da ita wajen tara da tura kuɗaɗen gudanar da ayyukan ta’addanci.
Hukumar ta kuma bayyana cewa masu ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci na buɗe asusun banki da sunayen mata, tare da amfani da lambobin waya wajen harkokin banki ta wayar salula ko karɓar sanarwar asusu, waɗanda ba a yi musu rajista da sunan mai asusun ko ainihin wanda ke amfana da kuɗin ba.
Yayin da take sanar da ’yan Najeriya kan ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da ɗaukar nauyin ta’addanci da sauran hanyoyin fitar da kuɗaɗen haram, NFIU ta ce sabon tsarin da ake shirin kafawa zai ƙara inganta haɗin gwiwa da masu ruwa da tsakin da aka ambata.
Sanarwar ta ce: “Najeriya ta ɗauki wani muhimmin mataki wajen ƙarfafa inganci da juriyar tsarin kuɗinta, yayin da NFIU ta tattaro manyan masu ruwa da tsaki domin taimakawa wajen tsara sabon tsarin musayar bayanan leƙen asirin kuɗi.
“Manufar wannan shiri ita ce ƙirƙirar wani amintaccen dandali da hukumomin gwamnati da cibiyoyi masu zaman kansu za su iya yin aiki tare yadda ya kamata domin gano sabbin barazana, dakile hanyoyin sadarwar kuɗaɗen haram da kuma ƙarfafa ingancin tsarin kuɗin Najeriya.”
Da yake wakiltar Babbar Daraktar NFIU, Hafsat Abubakar Bakari, Lauyan Janar na sashen, Felix Obiamalu, ya ce tattaunawar ta nuna an sauya daga tattaunawa kan shirin zuwa tsara shi da kuma fara aiwatar da shi.
Obiamalu ya ce:
“Mun wuce daga tattaunawa zuwa tsarawa, sannan zuwa ɗaukar alƙawari da aiwatarwa. Manufar yanzu ba wai kawai mu tattauna batun ba ce. Muna son mu tsara tare da juna yadda wannan haɗin gwiwa zai kasance, yadda zai gudana, irin amfanin da zai samar da kuma yadda za a tabbatar da dorewarsa a nan gaba.”
Ya ce an tsara haɗin gwiwar musayar bayanan leƙen asirin kuɗi ne domin samar da amintaccen dandali da hukumomin gwamnati da cibiyoyi masu zaman kansu za su yi amfani da shi wajen musayar muhimman bayanan leƙen asiri yadda ya kamata, tare da ƙarfafa martanin Najeriya kan ƙara ƙwarewar masu aikata laifukan kuɗi.