Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeAmurka ta gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 25 da harin...

Amurka ta gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 25 da harin 9/11

Amurka ta gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 25 da hare-haren ta’addancin 11 ga Satumba, 2001, inda aka kashe kusan mutane 3,000. An shirya tarukan tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a sassa daban-daban na ƙasar.

Amurka ta gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 25 da hare-haren ta’addancin 11 ga Satumba, 2001, inda aka kashe kusan mutane 3,000. An shirya tarukan tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a sassa daban-daban na ƙasar.

A birnin New York, iyalan wadanda suka mutu sun hallara a 9/11 Memorial Plaza, inda suka karanta sunayen wadanda aka kashe a hare-haren 2001 da kuma harin World Trade Center na 1993.

An gudanar da bikin ne tare da yin shiru sau bakwai domin tunawa da lokutan da jiragen sama suka kutsa cikin gine-ginen World Trade Center, lokacin da hasumiyoyin suka rushe, da hare-haren Pentagon da kuma faduwar Flight 93 a Pennsylvania.

A Washington, Shugaba Donald Trump ya shirya halartar bikin tunawa da harin a Pentagon, yayin da sauran manyan jami’an Amurka, ciki har da tsofaffin shugabanni da jagororin birnin New York, ake sa ran za su halarci bukukuwan.

A Pennsylvania ma an gudanar da bikin tunawa da fasinjoji da ma’aikatan jirgin Flight 93 da suka mutu bayan da aka yi garkuwa da jirgin. A fadin Amurka, an shirya wasu taruka domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu da kuma cika shekaru 25 da daya daga cikin munanan hare-haren da suka taba faruwa a tarihin ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments