Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Najeriya, Mohammed Idris, ya yi kira ga shugabannin addinai da su guji bayyana matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a ƙasar a matsayin yaƙin addini.
Ya ce irin wannan furuci na iya ƙara raba kan al’umma, tare da kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan Najeriya, musamman yayin da ake gab da zaɓen shekarar 2027.
Ministan ya kuma buƙaci shugabannin Kirista da su yi amfani da matsayinsu wajen yaɗa saƙonnin gaskiya, zaman lafiya, haƙuri da kishin ƙasa a tsakanin al’umma.
Mohammed Idris ya jaddada cewa bai kamata a kai wa wani ɗan Najeriya hari ko nuna masa wariya saboda addininsa ko imaninsa ba, yana mai kira ga ’yan ƙasa su rungumi haɗin kai domin ci gaban ƙasa.