Hukumar Shige da Fice ta Najeriya(NIS) ta kama wasu mutane biyu a Jihar Adamawa tare da tsabar kuɗi har Naira miliyan 34, waɗanda ake zargin suna da alaƙa da masu garkuwa da mutane.
Konturolan Hukumar Shige da Fice na Jihar Adamawa, Sani Sule-Jega, ne ya bayyana hakan ranar Laraba yayin wani taron manema labarai a Yola, babban birnin jihar.
Ya ce an kama mutanen biyu ne a wani samame da jami’an hukumar suka gudanar, inda binciken farko ya nuna cewa sun yi iƙirarin an tanadi kuɗin ne domin biyan fansa don kuɓutar da wani ɗan’uwansu da aka yi garkuwa da shi.
Sule-Jega ya ce hukumar ta miƙa mutanen biyu tare da kuɗaɗen da aka ƙwato ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya domin ci gaba da bincike da gano gaskiyar lamarin.
A wani samame na daban kuma, jami’an Hukumar Shige da Fice sun kama baƙin-haure 17 da ake zargin suna zaune a Najeriya ba tare da takardun izinin zama ba.
An kama mutanen ne a wani gida mai ɗakuna uku da ke unguwar Rumde Baruwa, a Ƙaramar Hukumar Yola ta Arewa.
A cewar Konturolan hukumar, daga cikin mutanen 17, akwai ’yan ƙasar Kamaru 13, waɗanda suka haɗa da maza takwas da mata biyar, yayin da sauran mutum huɗu ’yan ƙasar Chadi ne.
Hukumar ta ce tana ƙara tsaurara matakan sa ido tare da amfani da bayanan sirri domin gano hanyoyin da baƙin-haure ke bi wajen shiga ko zama a Najeriya ba bisa ƙa’ida ba.
Sule-Jega ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan tare da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanan da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Jihar Adamawa.