Wani jigo a jam’iyyar PDP, Lere Olayinka, ya ce zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 zai fi sauƙi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu idan aka kwatanta da zaɓen 2023.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Olayinka ya danganta hakan da dabarun siyasar Tinubu da kuma yadda ya samu goyon bayan wasu fitattun ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa.
A cewarsa, Tinubu ya yi nasarar jawo wasu manyan ’yan siyasar adawa zuwa cikin gwamnatinsa, lamarin da ya rage ƙarfi da tasirin jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.
Ya ba da misalin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, wanda duk da kasancewarsa ɗan jam’iyyar PDP, ke aiki tare da gwamnatin Shugaba Tinubu.
Olayinka ya ce da ba Wike yana aiki tare da gwamnatin Tinubu ba, da zai iya amfani da tasirinsa wajen ƙara wa PDP ƙarfi da kuma samun ƙarin goyon baya a zaɓen 2027.
Ya kuma ambaci Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, yana mai cewa tasirin manyan ’yan siyasa da sauye-sauyen goyon baya tsakanin jam’iyyu na iya taka muhimmiyar rawa a zaɓen 2027.
A cewarsa, yadda Tinubu ke gina alaƙa da ’yan siyasa daga ɓangarori daban-daban ya taimaka wajen ƙara masa ƙarfin siyasa gabanin babban zaɓen 2027.