Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiFBI ta tabbatar da taɓa binciken Tinubu kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

FBI ta tabbatar da taɓa binciken Tinubu kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taɓa kasancewa cikin binciken hukumomin Amurka kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi da halasta kuɗaɗen haram a farkon shekarun 1990. Batun ya sake kunno kai bayan Tinubu ya nemi kotun Amurka ta hana fitar da wasu bayanan FBI da DEA da suka shafi binciken.

Bayanan sun haɗa da fayil ɗin FBI da takardun tambayoyi na shekarun 1992 zuwa 1993, da kuma shari’ar kwace kusan dala 460,000 daga asusun da ke da alaƙa da Tinubu.

Sai dai, shari’ar ta kasance ta kwace kadarori ne (civil forfeiture), ba shari’ar da aka gurfanar da Tinubu kan safarar miyagun ƙwayoyi ba. Ba a samu hukuncin da ya tabbatar da cewa ya aikata laifin ba.

A yanzu, Aaron Greenspan na neman a saki ƙarin bayanan binciken ta hanyar dokar FOIA, yayin da Tinubu da lauyoyinsa ke neman a hana sakin bayanan, suna kare haƙƙinsa na sirri.

SourceDW Hausa
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments