Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiFadar Shugaban Ƙasa ta kashe N37.6bn kan tafiye-tafiye cikin shekaru 3

Fadar Shugaban Ƙasa ta kashe N37.6bn kan tafiye-tafiye cikin shekaru 3

Wani bincike kan bayanan kashe kuɗin gwamnati ya nuna cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta kashe N37.64bn kan tafiye-tafiyen cikin gida da na ƙasashen waje da sauran kuɗaɗen da suka shafi zirga-zirgar Shugaba Bola Ahmed Tinubu tsakanin Yuni 2023 zuwa Afrilu 2026.

Wani bincike kan bayanan kashe kuɗin gwamnati ya nuna cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta kashe N37.64bn kan tafiye-tafiyen cikin gida da na ƙasashen waje da sauran kuɗaɗen da suka shafi zirga-zirgar Shugaba Bola Ahmed Tinubu tsakanin Yuni 2023 zuwa Afrilu 2026.

Bayanan da GovSpend ta tattara sun nuna cewa an kashe N9.18bn a rabin shekarar 2023, N25.26bn a 2024, N2.7bn a 2025, sannan N477.4m tsakanin Janairu da Afrilu 2026. Mafi yawan kuɗin da aka kashe a 2024 ya shafi kuɗin canjin waje da kuma jiragen Fadar Shugaban Ƙasa.

Binciken ya kuma nuna cewa Tinubu ya yi tafiye-tafiyen ƙasashen waje 51 tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu 2023, inda ya ziyarci aƙalla ƙasashe 30 kuma ya shafe kusan kwanaki 261 a wajen Najeriya. Tafiyarsa ta baya-bayan nan zuwa Turai domin hutun makonni uku ta ƙara adadin zuwa 52.

A bangare guda, bayanan GovSpend sun nuna cewa an fitar da dala $553,884 domin tafiye-tafiyen Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, zuwa Amurka, Mozambique, Habasha, Birtaniya da Faransa tsakanin 2023 da 2024. An ce kuɗin ya kai N700.7m bisa farashin canjin da aka yi amfani da shi lokacin sayen kuɗin.

Sai dai wani mai rajin tabbatar da gaskiya, Ayo Ologun, ya yi kira da a binciki tushen da kuma dalilin kashe kuɗin gwamnati kan tafiye-tafiyen Uwargidan Shugaban Ƙasa, yana mai cewa ofishin First Lady ba ya cikin tsarin doka ko kasafin kuɗin ƙasa.

Haka kuma, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya soki lokacin da Tinubu ya tafi hutun makonni uku a Turai, yana cewa Shugaban ya bar Najeriya a lokacin da ake fama da tsadar man fetur, tsadar sufuri da matsalar tsaro. Sai dai mai bai wa Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce hutun ya zama dole domin Shugaban ya samu damar “sabunta ƙarfi”, yayin da zai ci gaba da karɓar rahotannin harkokin ƙasa daga jami’ansa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments