An ceto wata jaririyar da aka ce an watsar da ita cikin kwali a dajin Ashar da ke Wuese, Ƙaramar Hukumar Konshisha a Jihar Benue, bayan wani mazaunin yankin ya gano ta da rai.
Rahotanni sun ce jaririyar ta shafe kusan kwanaki uku a cikin dajin, an nannade ta da kaya sannan aka saka ta cikin kwali. An kuma gano tsutsotsi a jikinta tare da wari mai ƙarfi da ke fitowa daga kwali.
Wata mazauniya, Mrs Mbakasev Yisa, ce ta gano jaririyar a ranar Asabar bayan ta ji alamun motsi daga cikin kwali. An sanar da ’yan sanda, sannan aka kai jaririyar neman kulawar likita.
An ce jaririyar tana cikin mawuyacin hali, inda wani asibiti na farko ya kasa karɓarta. Daga bisani aka kai ta Dooshima Clinic da ke Wuese, inda aka kwantar da ita domin samun kulawar gaggawa.
Sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benue, DSP Peter Aondongu, ya ce rundunar ba ta samu rahoton hukuma kan lamarin ba. Ya ce ya tuntubi DPO na Konshisha, wanda ya bayyana cewa bai da masaniya kan faruwar lamarin.