Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiCin hanci na rage amincewar jama’a da ‘yan sanda — Bincike

Cin hanci na rage amincewar jama’a da ‘yan sanda — Bincike

Wani sabon bincike ya gano cewa cin hanci da rashin da’a tsakanin wasu jami’an ‘yan sanda na rage amincewar jama’a da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF).

Wani sabon bincike ya gano cewa cin hanci da rashin da’a tsakanin wasu jami’an ‘yan sanda na rage amincewar jama’a da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF).

Binciken, wanda James Ojo Adakole ya gudanar kan mutane 256, ya nuna cewa kashi 84.8 cikin 100 sun ce cin hanci da rashin da’a na rage musu amincewa da ‘yan sanda.

Haka kuma, kashi 62.9 cikin 100 ba su yarda ‘yan sanda za su iya kare rayuka da dukiyoyinsu ba, yayin da kashi 72.7 cikin 100 ba su da kwarin gwiwa kan yadda rundunar ke tunkarar barazanar tsaro.

Sai dai kashi 74.6 cikin 100 sun ce za su kai rahoton ayyukan da ake zargi, yayin da kashi 84.4 cikin 100 suka ce za su iya ba da bayanan tsaro masu amfani.

Binciken ya ce tsoron cin zarafi da rashin kare sirrin masu ba da bayanai na hana jama’a haɗin kai da ‘yan sanda. Mai binciken ya bukaci rundunar ta inganta ɗabi’a, horo da hulɗa da jama’a tare da tabbatar da kare bayanan sirri.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments