Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMalamin Musulunci ya gargadi ’yan siyasa kan alkawarin dawo da tallafin man...

Malamin Musulunci ya gargadi ’yan siyasa kan alkawarin dawo da tallafin man fetur

Wani malamin addinin Musulunci kuma tsohon mai ba wasu tsofaffin gwamnonin Kaduna shawara, Sheikh Haliru Maraya, ya gargadi ’yan siyasar da ke neman takara a zaɓen 2027 da su guji yi wa ’yan Najeriya alkawuran da ba za su iya cikawa ba.

Maraya ya yi wannan magana ne a Kaduna yayin da yake mayar da martani kan kiraye-kirayen da wasu ’yan siyasa ke yi na a dawo da tsarin tallafin man fetur da aka cire.

Malamin ya ce halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a yanzu ba ya ba da damar sake ɗaukar nauyin tallafin man fetur kamar yadda aka yi a baya, yana mai gargadin cewa hakan na iya ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin matsala.

Ya bukaci ’yan takarar shugaban ƙasa da sauran ’yan siyasa da su kasance masu gaskiya wajen bayyana wa ’yan Najeriya irin abubuwan da gwamnati za ta iya cimmawa, maimakon yin alkawuran da suka san ba za su iya cikawa ba domin samun ƙuri’u.

A cewarsa, dawo da tallafin man fetur zai buƙaci gwamnati ta ware makudan kuɗaɗe, waɗanda za a iya amfani da su wajen samar da ababen more rayuwa da sauran ayyukan ci gaba.

Maraya ya ce alkaluman da ake da su sun nuna cewa Najeriya na amfani da man fetur tsakanin lita miliyan 47 zuwa 64 a kowace rana, yayin da jimillar kuɗin lita guda, ciki har da tacewa, sufuri, inshora da kuɗaɗen kwastam, ke kaiwa kusan Naira 1,218.

Ya ce idan gwamnati ta sake dawo da tallafin ba tare da samun ingantaccen tsarin da zai iya ɗaukar nauyin hakan ba, akwai yiwuwar tattalin arzikin ƙasar ya ƙara fuskantar matsin lamba.

Sheikh Maraya ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da kada su yi amfani da matsalolin tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta wajen yin alkawuran yakin neman zaɓe da ba su da tabbacin cika su.

Ya ce Najeriya na buƙatar shugabannin da za su kasance masu ƙarfin hali wajen faɗa wa ’yan ƙasa gaskiya game da halin da tattalin arzikin ƙasar yake ciki.

Bugu da ƙari, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali wajen gyara matatun man fetur na cikin gida da kuma gina sababbi, domin rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments