Wasu ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa Funtua, a kusa da garin Tsafe da ke Jihar Zamfara, inda ake zargin sun yi awon gaba da wasu matafiya.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, inda mahara suka tare hanyar tare da bude wuta.
Wani matafiyi da ya tsallake harin ya bayyana cewa ’yan bindigan sun kai hari kan wata motar Sharon, inda suka tafi da mutanen da ke cikinta.
Haka kuma, an ce ’yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutanen da ke cikin wata tankar man fetur da ke kan hanyar.
Mazauna yankin sun tabbatar da jin karar harbe-harbe mai yawa a lokacin da lamarin ke faruwa, wanda ya dauki wani lokaci kafin jami’an tsaro su samu damar shiga tsakani.
Bayan harin, an ga wata motar Sharon da wata tankar mai a kan hanya, kofofinsu a bude, yayin da babu wani mutum a cikinsu.
An kuma ga kayayyakin wasu fasinjoji a cikin motocin.
Jami’an tsaro sun yi nasarar share hanyar tare da bai wa wasu matafiya damar wucewa zuwa Tsafe.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da ake zargin an yi garkuwa da su ba, ko kuma halin da suke ciki.
Haka kuma, an ruwaito cewa an ga wata mota ta kife a wurin da harin ya faru.
Har zuwa lokacin fitar da rahoton, ba a samu tabbacin hukumomin tsaro kan adadin mutanen da aka sace ko kuma wadanda suka jikkata ba.