Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiGwamnatin tarayya ta gargadi yankuna 915 kan barazanar ambaliyar ruwa

Gwamnatin tarayya ta gargadi yankuna 915 kan barazanar ambaliyar ruwa

Gwamnatin Tarayya ta gargadi yankuna 915 da ke cikin jihohi 19 da Abuja kan yiwuwar fuskantar babban haɗarin ambaliyar ruwa tsakanin 27 ga Agusta zuwa 9 ga Satumba, 2026.

Cibiyar Tsarin Gargadin Farko kan Ambaliyar Ruwa ta Ƙasa ce ta fitar da sabon rahoton, inda ta buƙaci al’ummomin da abin ya shafa su ɗauki matakan kariya cikin gaggawa.

Rahoton ya nuna cewa yankuna 429 a jihohi bakwai na cikin babban haɗari, yayin da yankuna 656 a jihohi 13 ke cikin matsakaicin haɗarin ambaliya.

Jihohin da aka lissafa cikin wuraren da ke cikin haɗari sun haɗa da Kogi, Benue, Rivers, Edo, Delta, Cross River, Bayelsa, Akwa Ibom, Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu, Imo, Ekiti, Lagos, Ogun, Ondo, Osun da Oyo.

Wasu daga cikin manyan biranen da aka bayyana suna cikin haɗarin sun haɗa da Lokoja, Makurdi, Fatakwal, Benin City, Asaba, Calabar, Yenagoa, Uyo, Aba, Onitsha, Enugu, Owerri, Lagos Island, Abeokuta, Akure, Osogbo da Ibadan.

Gwamnati ta danganta barazanar ambaliyar da yawan danshin ƙasa, ruwan sama mai yawa, saurin kwararar ruwa a saman ƙasa, cunkoson ruwa a magudanan ruwa da kuma karuwar ruwan koguna.

Ta buƙaci mazauna yankunan da ke cikin haɗari da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, tare da samar da hanyoyin kwashe jama’a idan buƙatar hakan ta taso.

Haka kuma, an shawarci jama’a da su guji zama, kasuwanci, ajiye motoci ko kayayyaki a bakin koguna, filayen ambaliya da sauran wuraren da ruwa ke taruwa.

Gwamnatin ta kuma umarci hukumomin bayar da agajin gaggawa, jami’an kula da muhalli da shugabannin al’umma da su ƙara sa ido kan koguna, magudanan ruwa, gadoji, madatsun ruwa da wuraren da ke fuskantar zaizayar ƙasa.

A gefe guda, Abuja da wasu yankuna na Nasarawa, Plateau, Bauchi, Borno, Gombe, Yobe, Zamfara, Sokoto, Katsina, Kano da Kaduna an sanya su cikin matakin matsakaicin haɗarin ambaliya.

Gwamnati ta yi gargadin cewa ci gaba da samun ruwan sama na tsawon lokaci na iya ƙara tsananta barazanar ambaliya a yankunan da ke cikin matsakaicin haɗari.

Ta buƙaci jama’a da su bi umarnin hukumomin bayar da agajin gaggawa, su nisantar da yara daga ruwan ambaliya, sannan su guji tuƙi ko tafiya a cikin ruwa mai gudana.

Haka kuma, an shawarci jama’a da su katse wutar lantarki idan ruwa na shirin mamaye gidaje, tare da kare magunguna, muhimman takardu, abinci da ruwan sha.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments