Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur.
Atiku ya ce idan gwamnati ta cire tallafin man fetur tare da samun kuɗaɗen da a baya ake kashewa wajen tallafawa farashin man, ya kamata ta bayyana wa ‘yan Najeriya yadda ake amfani da waɗannan kuɗaɗe.
Ya tambayi gwamnatin cewa: “Kun cire tallafi. Kun karɓi kuɗin da aka ce an ceta. To ina kuɗin suke?”
Atiku ya ce cire tallafin man fetur ya ƙara jefa ‘yan Najeriya cikin matsin tattalin arziki, sakamakon tashin farashin fetur, sufuri da sauran kayayyakin masarufi.
Ya kuma bayyana cewa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027, zai dawo da wani tsarin tallafi na musamman domin rage radadin tsadar rayuwa ga ‘yan Najeriya.
Sai dai mai magana da yawun Shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya zargi Atiku da sauya matsayinsa akai-akai kan batun dawo da tallafin man fetur.
Onanuga ya ce akwai bukatar Atiku ya yi cikakken bayani kan irin tsarin tallafin da yake son dawo da shi da kuma yadda gwamnati za ta iya ɗaukar nauyinsa ba tare da sake jefa tattalin arzikin ƙasar cikin matsala ba.
A nasa bangaren, Atiku ya ƙalubalanci gwamnatin da ta bincike shi tare da gurfanar da shi a kotu idan tana da hujjar cewa ya aikata wani laifi.
Ya ce tun bayan barinsa gwamnati a shekarar 2007, gwamnatoci daban-daban sun samu damar gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi masa, amma bai taba fuskantar tuhuma a gaban kotu kan waɗannan batutuwa ba.
Atiku ya ce yana fafatawa da “barayi” a 2027
Yayin da ake ƙara kusantar zaɓen 2027, Atiku ya ce yana shirin fafatawa da wasu ‘yan siyasa da ya kira “barayi”, yana mai cewa zai yi yaƙi da cin hanci da rashawa tare da gyara tattalin arzikin Najeriya.
APC ta mayar da martani, inda ta ƙalubalanci Atiku da ya je kotu ya gabatar da hujjoji kan zarge-zargen da yake yi ma wasu ‘yan siyasa, maimakon yin amfani da kalamai a lokacin kamfen.
Haka kuma, ƙungiyar daliban Najeriya ta NANS ta soki shirin dawo da tallafin man fetur, tana mai cewa dawo da tsohon tsarin ba tare da gyare-gyare ba na iya sake jefa tattalin arzikin ƙasar cikin matsala.
Atiku ya kuma yi magana kan shekarun Tinubu
A wani sabon ci gaba, Atiku ya yi ikirarin cewa yana da hujjojin da yake ganin za su tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya fi shekarun da aka fi sani da shi.
Atiku ya ce yana da hujjar da zai gabatar a kotu kan batun shekarun Shugaban ƙasar, yana mai cewa shi kansa yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana ganin ya dace ya ci gaba da neman shugabancin Najeriya.
Yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, batutuwan tallafin mai, tsadar rayuwa, shekarun Tinubu, tsaro da yadda ake tafiyar da dukiyar ƙasa na ci gaba da zama manyan batutuwan da ke rura wutar adawar siyasa tsakanin Atiku da gwamnatin Tinubu.