Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKwastam ta kama dabbobin daji da ake zargin ana safararsu ba bisa...

Kwastam ta kama dabbobin daji da ake zargin ana safararsu ba bisa ƙa’ida ba a Kano

Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Kano/Jigawa, ta kama wasu dabbobin daji da ake zargin ana safararsu ba bisa ƙa’ida ba, tare da cafke mutane uku a kan hanyar Kano zuwa Daura.

Hukumar ta ce an gudanar da samamen ne a ranar 25 ga Agusta 2026, bayan jami’anta sun samu sahihan bayanan sirri kan safarar dabbobin.

Mukaddashin Mataimakin Kwanturola mai kula da ayyukan yaƙi da fasa-kwauri, Muhammad Zanna, ya ce waɗanda ake zargin sun yi ƙoƙarin ba jami’an Kwastam cin hanci sau da dama domin su tsere wa hukunci, amma jami’an sun ƙi karɓar kuɗin.

Ya ce an mika dabbobin da kuma mutanen ukun da aka cafke ga jami’in kula da namun daji na musamman na hedikwatar hukumar domin gudanar da ƙarin bincike da ɗaukar matakin da ya dace.

Hukumar Kwastam ta ce kama dabbobin na daga cikin matakan da take ɗauka wajen yaƙi da safarar namun daji ba bisa ƙa’ida ba, musamman dabbobin da ke fuskantar barazanar bacewa, da kuma kare albarkatun halittu na Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments