Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTinubu ya yi alkawarin rage kudin sufuri daga Oktoba

Tinubu ya yi alkawarin rage kudin sufuri daga Oktoba

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatocin tarayya da jihohi sun ɗauki matakan rage kudin sufuri, ta hanyar amfani da motocin CNG da masu amfani da wutar lantarki.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatocin tarayya da jihohi sun ɗauki matakan rage kudin sufuri, ta hanyar amfani da motocin CNG da masu amfani da wutar lantarki.

Tinubu ya ce an kafa kwamiti na tarayya da jihohi da zai fara aiwatar da shirin nan take, inda ya yi alkawarin cewa daga 1 ga Oktoba ’yan Najeriya za su fara amfana da raguwar kudin sufuri.

Ya ce motocin CNG na kashe kashi 60 zuwa 80 cikin 100 ƙasa da motocin mai wajen sayen man fetur, yayin da sama da motoci 120,000 aka riga aka sauya su zuwa CNG a faɗin ƙasar.

Sai dai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki matakin, yana mai cewa alkawarin rage kudin sufuri ya zo ne sakamakon matsin lambar da shirin sa na dawo da tallafin man fetur ya haifar. Ya ce CNG na da amfani, amma ba zai iya magance matsalar tsadar rayuwa shi kaɗai ba.

A gefe guda, gwamnonin jihohi sun ce za su goyi bayan shirin National Affordable CNG Transit Programme (NACTP), wanda ke da nufin rage kudin sufuri. Sai dai masana tattalin arziki sun yi tambaya kan yadda za a samar da kudaden aiwatar da shirin, musamman ganin cewa wasu jihohi ba su tanadi irin wannan shiri a kasafin kuɗin shekarar 2026 ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments