Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabarai2027: Atiku ya yi alkawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin shekara daya

2027: Atiku ya yi alkawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin shekara daya

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Najeriya cikin shekara guda idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata hira da BBC Hausa, inda ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakan gaggawa domin inganta tsaro tare da rage yawan matasan da ke shiga aikata laifuka.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce zai ƙara yawan jami’an tsaro, tare da samar musu da kayan aiki da isasshen kuɗin gudanar da ayyukansu.

Ya kuma bayyana shirin samar da tallafi da damar kasuwanci ga matasa domin su samu sana’o’i da hanyoyin dogaro da kai, yana mai cewa rashin aikin yi na daga cikin abubuwan da ke iya jefa matasa cikin aikata laifuka.

Atiku ya ce idan aka ba shi damar jagorantar ƙasar, zai ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalar cikin shekara guda.

“Ba zan ɗauki fiye da shekara guda ba wajen kawo ƙarshen wannan matsala.

Za mu ɗauki matakan da suka dace kuma cikin shekara guda za mu kawo ƙarshen rashin tsaro, in Allah ya yarda,” in ji Atiku.

Ya kuma bayyana shirin tattaunawa da shugabannin ƙasashen Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) domin farfaɗo da rundunar ECOMOG da ƙarfafa haɗin gwiwar sojojin ƙasashen yankin.

A cewarsa, Najeriya za ta iya haɗa ƙarfi da ƙasashen Côte d’Ivoire, Saliyo da Laberiya wajen yaƙi da matsalar tsaro da dawo da zaman lafiya a yankin.

Dangane da alaƙar Najeriya da Nijar, Atiku ya ce juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar bai kamata ya zama dalilin da zai sa Najeriya ta katse alaƙar diflomasiyya da ita ba.

Ya ce Najeriya da Nijar suna da dadaddiyar alaƙa, musamman ganin kusancin da ke tsakanin al’ummomin ƙasashen biyu.

Atiku ya ƙara da cewa zai yi ƙoƙarin dawo da Nijar, Burkina Faso da Mali cikin ECOWAS domin ƙarfafa haɗin kan ƙasashen yankin da kuma taimakawa wajen rage matsalolin rashin aikin yi da rashin tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments