Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaYa kamata Tinubu da iyalansa su fara tattara kayansu daga Villa kafin...

Ya kamata Tinubu da iyalansa su fara tattara kayansu daga Villa kafin 2027 – Dino Melaye

Jagoran jam’iyyar ADC, Dino Melaye, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da iyalansa su fara tattara kayansu daga Fadar Shugaban Ƙasa, yana mai cewa jam’iyyar ADC za ta kayar da APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Melaye ya ce matsalolin yunwa, rashin tsaro, kashe-kashe da matsin tattalin arziki sun sa ’yan Najeriya ke ƙara nuna rashin gamsuwa da gwamnatin Tinubu.

Ya kuma zargi gwamnatin da gazawa wajen aiwatar da kasafin kuɗaɗe, tare da kasa biyan wasu kuɗaɗen kwangilolin da aka bayar.

Jagoran ADC ɗin ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce sakamakon zaɓen 2027 zai nuna burin ’yan Najeriya na ganin an samu sauyin gwamnati.

Haka kuma, Melaye ya zargi Shugaba Tinubu da yin kalaman da ke nuna cewa magudi, tashin hankali da satar ƙuri’u abin yarda ne a siyasa, yana mai cewa irin waɗannan kalamai ba su dace da matsayin shugaban ƙasa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments