Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSojojin Amurka sun fara horas da sojojin Najeriya kan amfani da jirage...

Sojojin Amurka sun fara horas da sojojin Najeriya kan amfani da jirage marasa matuki

Sojojin Amurka sun fara horas da sojojin Najeriya kan amfani da jiragen sama marasa matuƙi, kula da sojojin da suka samu raunuka a fagen daga da kuma wasu dabarun yaƙi.

An gudanar da horon ne a wani sansanin soji da ke jihar Bauchi, a wani ɓangare na shirin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Horarwar na da nufin ƙara wa sojojin Najeriya ƙwarewa, inganta shirye-shiryen yaƙi da kuma ƙarfafa ƙarfin haɗin gwiwar soji tsakanin ƙasashen biyu na dogon lokaci.

Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoto da Rundunar Sojin Amurka mai kula da Afirka (AFRICOM) ta fitar a ranar Litinin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments