Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeGuguwa ta raunata mutane 41 a Faransa

Guguwa ta raunata mutane 41 a Faransa

Wata mummunar guguwa mai ƙarfi ta ratsa ƙauyen Pomas da ke yankin kudu maso yammacin Faransa, inda ta raunata mutane 41 tare da lalata gidaje da dama.

Wata mummunar guguwa mai ƙarfi ta ratsa ƙauyen Pomas da ke yankin kudu maso yammacin Faransa, inda ta raunata mutane 41 tare da lalata gidaje da dama.

Rahotanni sun ce mutane 15 daga cikin waɗanda suka jikkata an kai su asibiti, ciki har da wata mata mai juna biyu da ta samu raunuka bayan rugujewar gidanta.

Guguwar, wadda aka ce iskar ta kai gudun kilomita 117 a cikin awa guda, ta tumbuke bishiyoyi, ta yayyaga rufin gidaje tare da lalata kusan gidaje 300. Hukumomi sun tura ma’aikatan agaji sama da 120 domin gudanar da ayyukan ceto da taimako.

Hukumomin Faransa sun kuma ce kusan gidaje 2,800 a ƙauyuka 10 sun rasa wutar lantarki sakamakon mummunan yanayin. An kuma samu cikas a harkokin sufuri, yayin da aka soke matakin gasar keke ta Vuelta a España a yankin bayan wata ƙaramar guguwa mai ƙanƙara ta tilasta wa ’yan tseren neman mafaka.

Hotunan da aka ɗauka a Pomas sun nuna bishiyoyin da suka faɗi, motoci da suka lalace da tarkacen gidaje da guguwar ta lalata. Haka kuma, an samu jinkiri da soke wasu jiragen sama a filayen jiragen sama da dama na Faransa.

Hukumar kula da yanayi ta Faransa, Météo-France, ta ce ƙasar tana fuskantar guguwar iska irin wannan sau da dama a kowace shekara. Wannan na zuwa ne yayin da Faransa da wasu sassan Turai ke fama da matsanancin zafi, gobarar daji da sauran sauye-sauyen yanayi a wannan bazarar.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments