Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa wasu daga cikin mutanen da aka saka cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na 2027 na fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa da ba a warware ba.
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana damuwarsa kan haɗa tsoffin jami’an gwamnati, ciki har da Betta Edu da Ngozi Olejeme, cikin kwamitin.
ADC ta buƙaci gwamnatin tarayya ta bayyana ko an kammala bincike ko kuma an warware zarge-zargen da ake dangantawa da mutanen da aka naɗa, ko kuma nadin nasu wata hanya ce ta yafewa waɗanda ake zargi da aikata laifukan rashawa.
Jam’iyyar ta kuma yi ikirarin cewa wasu daga cikin mambobin tawagar yaƙin neman zaɓen ba su da cikakken amincewar jama’a.
A cewar ADC, zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai kasance wata dama ga ’yan Najeriya wajen tantance yadda Shugaba Tinubu ya gudanar da mulkinsa cikin shekaru uku da suka gabata.