Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, ta cire dokar hana cire kuɗi daga asusun gwamnatin jihar Osun, bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a buɗe asusun.
Hukumar ta ce tana binciken yadda aka sarrafa kusan Naira biliyan 11, da suka haɗa da kuɗaɗen muhalli, tallafi da rabon kuɗin gwamnatin tarayya.
Bayan umarnin shugaban ƙasar, an tabbatar da cewa asusun gwamnatin Osun da ke bankunan First Bank da Zenith Bank sun koma aiki.